Gabon : Bongo, Ya Koma Morocco Don Ci Gaba Da Jinya
Shugaba Ali Bongo Odimba na Gabon, ya koma jinya a kasar Morocco, kasa da sa'o'i 24 bayan ya koma koma gida inda ya halarci bikin rantsar da sabuwar gwamnati.
Shugaba Bongo, wanda ya kamu da rashin lafiya a ranar 24 ga watan Oktoba na 2018 data gabata a Saudiyya, ko koma a birnin Rabah na kasar Morocco inda yake ci gaba da karbar magani.
A safiyar ranar Talata, shugaba Bongo, ya halarci bikin rantsar da sabuwar gwamnatins amai ministoci 38 a fadar shugaban kasar dake Libreville, saidai bikin ba'a gayyaci jama'a da 'yan jarida a bikin ba.
'Yan kasar dai sun samu ganinshi a wani faifan bidiyo da kafofin yada labarai na kasar suka wallafa.
Komawarsa gida na zuwa ne kwanaki kadan bayan yunkurin yujin mulkin da akayi wa gwamnatinsa,.wanda baiyi nasara ba.