Buhari Ya Bukaci Taimakon Mutanen Don Gano Barayin Kudaden Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34840-buhari_ya_bukaci_taimakon_mutanen_don_gano_barayin_kudaden_gwamnati
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon mutanen kasar don gano barayin kudaden jama'a.
(last modified 2019-01-17T11:56:43+00:00 )
Jan 17, 2019 11:56 UTC
  • Buhari Ya Bukaci Taimakon Mutanen Don Gano Barayin Kudaden Gwamnati

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci taimakon mutanen kasar don gano barayin kudaden jama'a.

Kamfanin dillancin labaran NAN na tarayyar Najeriya ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake tattaunawa ta  musamman kuma kai tsaye da  wata gidan Talabijin ta kasar. 

Shugaban yana amsa tambayoyi ne a shiri mai sunan "The Candidates" , inda aka tambayeshi dangane da zargin da ake yiwa gwamnatinsa na rashin gurfanar da yan jam'iyyarsa ta APC wadanda ake zargi da sama da fada da kudaden jami'a, musamman tsohon sakataren gwamnati wanda har sai da aka sauke shi daga mukaminsa sanadiyar zargin. 

Shugaban ya musanta wannan zargin ya kuam kara da cewa hatta shi tsohon sakataren gwamnati Mr Babachir David Lawal, hukumar EFCC tana bincike a kan lamarinsa kuma a duk lokacinda ta sami wani dalili na hukuntashi to kuwa  za'a gurfanar da shi a gaban kotu. 

Shugaban ya kammala da cewa a irin tsarin mulki na yanzu ba zai yu a kama mutane a zufa a gidajen yari ba tare da ana da kwakwarar hujja na cewa suna da laifin da suka aikata ba.