Jan 18, 2019 06:43 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar Sudan

Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa a jiya Alhamis ma masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Umar Hassan Albashir sun sake fitowa a kan titunan birnin Khartun babban birnin kasar, inda jami'an tsaro suka tarwatsasu da hayaki mai sa hawaye.

Majiyar muryar JMI daga sudan ta bayyana cewa masu zanga- zanga a birnin Khartum sun taru a wani dangali a tsakiyar kasar, inda daga nan suka nufi fadar shugaban kasar suna rara taken kin jinin gwamnati, amma jami'an tsaro na yansanda suka sha gabansu suka kuma tarwatsau da hayaki mai sa hawaye. 

wasu majiyoyin sun bayyana cewa a fafatarwar na jiya tsakayin mazu -zanga zanga da jami'an tsaron kasar ta Sudan mutun guda ya rasa ransa. 

Banda haka wasu rahotannin sun bayyana cewa an gudanar da Irin wannan zang-a zangar a garuruwa da dama a fadin kasar. 

Tags