Tarayyar Afrika Ta Bayyana Tababanta Kan Sakamakon Zaben Kasar Congo
(last modified Fri, 18 Jan 2019 06:44:27 GMT )
Jan 18, 2019 06:44 UTC
  • Tarayyar Afrika Ta Bayyana Tababanta Kan Sakamakon Zaben Kasar Congo

Kungiyar tarayyar Afrika ta bayyana damuwarta da sakamakon zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a kasar Kongo Kinshasa.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ta nakalto shugaban komitin zartarwa na kungiyar Musa Faki Mahama yana fadar haka a jiya Alhamis. 

Faki ya kara da cewa duk da cewa a halin yanzu babu wani tashin hankali a kasar Kongo bayan zaben ranar 30 ga watan Decemban da ya gabata, amma kuma sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta bayyana ya jefa kasar cikin zullumi, don bangarori da dama basu amince da sakamakon zaben ba, kuma suna ganin ba shine sakamakon zaben na gaskiya ba. 

Hukumar zaben kasar dai ta bayyana Felix Tshesekedi a matsayin wanda ya lashe zaben, amma kuma a bangare guda kungiyar malaman kiristocin kasar suna ganin sakamakon bai yi dai dai da wannan masu sanya idonsu suka fada masu ba, suna ganin wani dan jam'iyyar adawar kasar ne mai Suna Martin Fayulu ya lashe zabe.

Wasu kuma suna ganin wata yerjejeniya ce , a asirci Felix ya kulla da gwamnatin Josrept Kabila. A ranarb 30 ga watan Decemban da ta gabata ce aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Kongo DMC sannan shi ne zabe na farko da ake saran wata gwamnatin farar hula zaya mikawa wata farra hula tun bayan samun 'yencin kan kasar .