Tarayyar Afirka Tana Da Shakku Akan Sakamakon Zaben Kasar Demokradiyyar Congo
Shugaban cibiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya fada a jiya Alhamis cewa; Da akwai shakku mai yawa akan sakamakon zaben jamhuriyar Demokradiyyar Congo da aka yi a watan Disamba
Faky Muhammad ya kara da cewa; Tare da cewa abin farin ciki ne da akwai zaman lafiya a halin yanzu a kasar ta Demokradiyyar Congo, sai dai har yanzu da akwai damuwa
Faky Muhammad ya bayyana haka ne a wurin bude taron shugabannin kasashen tarayyar Afirka a birnin Adis Ababa na kasar Habasha
Daga cikin mahalarta taron da akwai Shugaban riko-riko na kungiyar Paul Kagame wanda shi ne shugaban kasar Rwanda, sai kuma shugabannin kasashen Afirka ta kudu, Zambia, Namibia, Uganda, COngo, Habasha, Gunea da kuma Chadi.
Hukumar zaben kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta bayyana Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben.