An Gudanar Zanga-Zangar Goyon Bayan Marzia Hashimi A Najiriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34859-an_gudanar_zanga_zangar_goyon_bayan_marzia_hashimi_a_najiriya
Wasu Musulmi a tarayyar Nageriya sun yi ta naga hotunan Marzia Hashimi 'yar jaridan nan ta Presstv wacce aka kama a Amurka a kwanakin da suka gabata tare da bukatar a sake ta.
(last modified 2019-01-19T03:07:59+00:00 )
Jan 19, 2019 03:07 UTC
  • An Gudanar Zanga-Zangar Goyon Bayan Marzia Hashimi A Najiriya

Wasu Musulmi a tarayyar Nageriya sun yi ta naga hotunan Marzia Hashimi 'yar jaridan nan ta Presstv wacce aka kama a Amurka a kwanakin da suka gabata tare da bukatar a sake ta.

Majiyar muryar JMI ta bayyana cewa an kama Marzia Hashimi ne a lokacinda ta isa tashar jiragen sama na St. Louis na kasar Amurka a ranar Lahadin da ta gabata ba tare da an bayyana mata irin laifin da ta aikata ba. 

Hukumar FBI ta kasar Amurka ce ta kama Marziya Hashimi wacce,  bakar fata ce musulma yar kasar ta Amurka, wacce kuma ta musulunta bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan Iran. Marziya tana da shahadar karatun aikin jirida a kasar ta Amurka.  

Ta zo kasar iran kimani shekaru 25 da suka gabata, inda ta yi karatun addini,  sannan aiki da tashar Talabijin ta Presstv wacce take watsa shirye-shiryenta da harshen turanci a nan birnin Tehran.  

Iyalanta sun bayyana cewa jami'an hukumar FBI sun kamata ne a lokacinda tage ganin dangi da yan uwa a kasarta. 

Shugaban hukumar gidajen radiyo da telebijin a nan kasar Iran Ali Askari ya yi allawadai da kama yar jaridan, ya kuma bukaci a gaggauta sakinta.