DR Congo Ta Yi Watsi Da Bukatar Kungiyar (AU)
-
Kakakin gwamnatin kasar ta DR Congo, Lambert Mende. AFP/GETTY IMAGES
Gwamnatin jamhuriya Demokuradiyyar Congo, ta yi watsi da bukatar kungiyar tarayya Afrika (AU), wacce ta nemi da a dakatar da fitar da sakamakon zaben shugaban kasar na dindindin.
Kungiyar ta (AU), ta ce tana dai tana da shakku, akan sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta sanar wanda ya bayyana dan takara Félix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 38%.
Da yake maida martaki kan bukatar kungiyar ta (AU), kakakin gwamnatin kasar ta DR Congo, Lambert Mende, ya ce kotun tsarin mulkin kasar tana da cikaken 'yancin da ba zata yi aiki da bukatar da kungiyar tarayyar Afrika ta yi ba.
A wani lokaci yau Litini ne ake sa ran wata tawagar kungiyar ta AU, da shugabanta na wannan karo kana shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame, da wasu shugabannin Afrika zata isa a Kinshassa babban birnin kasar ta DR Congo domin taimaka wa kasar wajen warware kiki-kakar da ya biyo bayan zaben.
Saidai kakakin gwamantin kasar ta DR Congo, Mr Mende ya ce kasar tana maraba da zuwan tawagar, amma a cewarsa ba za'a canza yadda ake tafitar da al'amuran bayan zaben ba.
A wani labari kuma dan takaran adawa da ya zo na biyu a zaben shugaban kasar, Martin Fayulu, ayyana kansa ya yi a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da ya bukaci kotun tsarin mulkin kasar, data soke sakamakon zaben tare da sake kidayar kuri'u.