Madagaska : Rajoelina, Ya Yi Rantsuwar Kama Mulki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34869-madagaska_rajoelina_ya_yi_rantsuwar_kama_mulki
A Madagaska, yau Asabar ne zababen shugaban kasar, Andry Rajoelina, ya yi rantsuwar kama aiki a wani babban biki da aka gudanar da filin kwallon kafa na Antananarivo babban birnin kasar.
(last modified 2019-01-19T15:27:26+00:00 )
Jan 19, 2019 15:27 UTC
  • Madagaska : Rajoelina, Ya Yi Rantsuwar Kama Mulki

A Madagaska, yau Asabar ne zababen shugaban kasar, Andry Rajoelina, ya yi rantsuwar kama aiki a wani babban biki da aka gudanar da filin kwallon kafa na Antananarivo babban birnin kasar.

An gudanar da bikin tare da halartar manyan baki da suka hada da shuwagabannin kasashen duniya da dama.

Daga cikin da akwai shuwagabannin kasashen Afrika shida da suka hada dana (Guinea, Ghana, Zambiya, Namibiya, Comoros, da kuma Habasha), baya ga hakan kuma akwai shuwagabbin manyan kamfanoni da attajirai na duniya da kuma tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.

Bikin ya kuma samu halartar sauren 'yan takaran da suka fafata da sabon shugaban kasar a zabe.

A cikin wajabinsa bayan rantsarda dashi, Andry Rajoelina, ya bayyana matukar jin dadinsa akan yadda a cewarsa a karon farko aka mika mulki cikin ruwan sanyi a cikin tarihi a kasar.

Sabon shugaban, ya kuma yi alkawarin, samar da ci gaba a kasar, duba da koma bayan shekaru biyar data fuskanta a wannan fanni, ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa.

Mista Rajoelina ya dai lashe zaben ne da kashi 55,65% na yawan kuri'un da aka kada, a yayinda babban aboklin hammayarsa Marc Ravalomanana ya samu kashi 44,34%.

Da yammacin yau Litini ne ake sa ran zai bayyana sunan sabon fira ministansa.