Najeriya : Buhari Ya Shirya Yin Magudi A Zabe_Obasanjo
-
Wannan ba shi ne karo na farko ba da tsohon shugaban kasar ta Najeriya, Olusegun Obasanjo, ke sukan shugaba Buhari ba
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da shirya magudi domin lashe babban zaben kasar dake tafe.
Cif Obasanjo, wanda ke bayyana hakan a cikin wata wasika, ya ce shugaba Buhari yana aiki da jami'an tsaro da kuma manyan jami'an hukumar zabe domin ya samu nasara da gagarimin rinjaye a zaben da za'a gudanar a watan gobe.
Tuni dai fadar shugaban kasar ta mayar da martani kan kallaman tsohon shugaban kasar, tana mai danganta su da abun mamaki da takaici, hasali ma a cewarta ''wauta ne''.
A sanarwar data fitar fadar shugaban kasar, ta ce zaben na watan Fabrairu za'a gudanar dashi cikin haske da adalci, kamar yadda shugaba Buhari ya yi alkawari wa 'yan kasar da duniya.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da tsohon shugaban kasar ta Najeriya, Olusegun Obasanjo, ke sukan shugaba Buhari ba, wanda ya mara wa baya a waccen zaben na 2015.
Idan ana tune a watan Janairu 2018, Obansanji, ya bayyana a cikin wata budadiyar wasika cewa, bai kamata Buhari ya sake neman wani wa'addin mulki ba.
'Yan takara 72 ne zasu fafata a zaben na ranar 16 ga watan Fabrairu mai zuwa, ciki har da shugaba Muhammadu Buhari karkashin jam'iyyar APC mai mulki, da kuma babban abokin hammayarsa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, na lokacin mulkin Olusegun Obasanjon, tsakanin shekara 1999 zuwa 2007.