Jan 21, 2019 04:39 UTC
  • Mun Kashe Sojojin Chadi, Saboda Ziyarar Firaministan Isra'ila_AQMI

Kungiyar Al-Qaïda, reshen kasashen larabawa na Magreb, (Aqmi), ta dauki alhakin kai mummunan harin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin tawagar MDD, na kasar Chadi guda goma da raunata wasu 25.

Kungiyar ta Aqmi, ta ce ta kai harin ne saboda ziyarar da fira ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kai a kasar Tchadi, a cewar kamfanin dilancin labaren Al-Akhbar, na Mauritaniya, da yayi kaurin suna wajen bayyana harkokin kungiyar.

A jiya Lahadi ne firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kai ziyara birnin N'Djamena na kasar Chadin inda ya gana da shugaban kasar Idriss Deby, wanda kuma suka sanar da dawo da huldar diflomatsiya a tsakaninsu bayan katseta na tsawon shekaru 47.

Harin wanda aka kai da sanyin safiyar jiya Lahadi, shi ne mafi muni da aka kai kan kan sojojin MDD, a kasar Mali, dake fuskantar barazanar mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

A wata sanarwa da babban sakatare na MDD, Antinio Guteres ya fitar, ya ce sojojin kasar Chadi 10 ne suka mutu a harin, kana wasu 25 suka raunana a harin da aka kai masu a yankin Aguelhok, dake arewa maso gabashin kasar Mali a kusa da iyaka da kasar Aljeriya, kuma sojojin sunyi nasara hallaka mayakan da dama.

Tags