Najeriya: Sojoji Sun Dakile Wani Harin Boko Haram A Buni-Yadi
Runduna ta 27 ta sojojin Najeriya da kuma sojoji a makarantar sojoji ta Musamman a Buni-Yadi na jihar Yobe a tarayyar Nageriya sun bada sanarwar dakli wani harin mayakan Boko Haram a kan sansaninsu da ke garin.
Manjo Nuraini Alimi darakta mai kula da hulda da jami'an na Rundunar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a jiya Lahadi kan cewa, mayakan boko haram sun kawo farmako kan makarantar sojoji ta musamman da ke Buni-yadi da misalin karfe 4:15 a jiya Lahadi, inda rundunar ta maida masu martani, ta kuma halaka da dama daga cikinsu, a yayinsa wasu suka tsira da raunuka a jikinsu.
Manjo Nuraini ya kara da cewa sojojin rundunar 4 n4 suka sami yan raunuka a fafatawar , kuma a halin yanzu suna jinya.
Daga karshe Nuraini ya tabbatar da cewa sojojin Rundunar suna cikin hali mai kyau don fuskantar makiya.