An Nada Sabon Pira Minista A Kasar Burkina Faso
Shugaban kasar ta Burkina Faso Rock Mark Christine Caboure ne ya sanar da Christophe Joseph Marie Dabire a matsayin sabon Pira Minista
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ba da labarin cewa; An sanar da sabon pira ministan ne kwanaki uku da Paul Kaba Thieba ya yi murabus saboda matsalar da kasar take fuskanta na hare-hare masu tsaurin ra'ayi
Gabanin nadin nashi,Christophe Joseph Marie Dabire ya wakilcin kasarsa a kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( Ecowas), kuma ya taba zama dan majalisa
Daga cikin mukaman da ya taba rikewa da akwai ministan kiwon lafiya daga 1992 zuwa 1997, sai kuma ministan ilimin kananan makarantu daga 1997 zuwa 2000.
A ranar juma'ar da ta gabata ne ofishin shugaban kasar ta Borkina Faso ya sanar da murabus din Paul Kaba daga mukamin Pira minista
A cikin watannin bayan nan kasar ta Borkina Faso tana fuskantar hare-haren masu tsaurin ra'ayi, abin da ya sa aka kafa dokar ko ta kwana a cikin wasu sassa na kasar, musamman akan iyaka da kasashen Mali da Nijar