Ghana Ta Dakatar Da Aikin Kamfanin China Na Hakar Ma'adanai
Hukumomi a kasar Ghana, sun dakatar da aikin kamfanin hakar ma'adanai na Shaanxi, mallakin kasar China a kasar.
Matakin dakatar da kamfanin ya biyo bayan wani mummunan hatsari da ya faru a wata mahakar zinari a arewacin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 16.
Bayannan da mahukuntan Ghana suka fitar, sun nuna cewa binciken da akayi ya gano cewa masu aikin a mahakar 16 sun mutu ne sanadin shakar wani iskar gas mai guba, bayan fashewar data auku a wani rame na mahakar.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba, da kamfanin na kasar China ke fuskantar irin wannan lamari ba, inda ko a shekaru biyu da suka gabata, kamfanin ya dakatar da aikinsa na watanni uku saboda rashin matakai na tsaro, inda wasu masu aiki a mahakar bakwai suka mutu a cikin irin wannan yanayi.
Ghana ita ce kasa ta biyu wajen samarwa da kuma fitar da zinari a Afrika, wanda manyan kamfanoni na kasa da kasa, da kuma masu bidar zinari ba bisa ka'ida ba ke gudanar da aikin.