Sudan:'Yan Adawa Sun Kira Zanga-Zanga
(last modified Fri, 25 Jan 2019 11:47:26 GMT )
Jan 25, 2019 11:47 UTC
  • Sudan:'Yan Adawa Sun Kira Zanga-Zanga

Kungiyoyin jam'iyun adawa a sudan sun bukaci al'ummar kasar da su gudanar da zanga-zanga bayan kamala sallar juma'a

Tashar talabijin din Alhadhas ta habarta cewa kungiyoyin fararen hula dake adawa da gwamnatin Sudan tare da manyan jam'iyun adawa uku na kasar sun bukaci al'umma da su fito dafifi domin gudanar da gagaruman zanga-zanga bayan kamala sallar juma'a na wannan rana 25 ga watan janairu.

Tun a ranar 19 Dicembar shekarar da ta gabata ce, al'ummar kasar suka fara gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da matsin tattalin arzikin da kasar ta fada ciki, musaman ma kara farashin kudin biredi da man fetir.

Hukumomin kasar Sudan sun ce ya zuwa yanzu, zanga-zangar da al'ummar kasar ke yi ya yi sanadiyar mutuwar 'yan adawa 24, to saidai kungiyoyin kare hakkin bil-adama na kasa da kasa sun dogara da wasu rahotani masu inganci, inda suka tabbatar da cewa mutanan da suka mutu sun haura zuwa 40.

A halin da ake ciki, zanga-zangar ta kiride zuwa neman kifar da gwamnatin Umar Al-Bashir wanda yake rike da ragamar milkin na Sudan tun a shekarar 1993.