An Kashe Masu Zanga -Zanga Biyu A Kasar Sudan
A ci gaba da zanga-zangar kin jinin gwamnatin wanda mutanen kasar Sudan suke yi an kara kashe wasu mutane biyu.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wata majiyar jami'an tsaron kasar Sudan tana fadar cewa an kashe mutane biyu a jiya Alhamis, a lokacinda suke zanga-zangar kin jinin gwamnati shugaba Umar Hassan Al-Bashir.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama dai sun bayyana cewa , tun lokacinda aka fara rikici a kasar Sudan a cikin watan Decemban da ya gabata an kashe mutane fiye da 40.
Sannan majiyar ma'aikatar cikin gida na kasar ta Sudan ta bayyana cewa tun lokacin da aka soma rigimar tana tsare da mutane 816.
Tun ranar 19 ga watan Decemban da ta gabata ce mutanen kasar Sudan suka fara zanga-zangar kin jinin gwamnati shugaban Umar Hassan Albashir, saboda tashin goran zabi da kayakin bukatun yau da kullum.
Wannan dai shi ne tashin hankali mafi muna wannan kasar Sudan take fuskanta tun fiye da shekaru 30 da suka gabata.