Najeriya : Buhari Ya Nada sabon Alkalin Alkalai
Shugaba Muhammadu Buhari a tarayyar Najeriya ya kori alkalin alkalan kasar Walter Annoghen daga aikinsa na wacin gadi kafin ya warware matsalarsa da kotun ladabatar da ma'aikata na kasa.
kamfanin dillancin labaran nan na tarayyar Najeriya ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake nada Justice Ibrahim Tanko wanda zai rike kujerar alkalin alkalan kasa zuwa abinda hali yayi.
A jawabinda shugaban ya karanta a lokacinda yake rantsar da Justice Ibrahim Tanko ya bayyana cewa rahoto ya zo masa daga kotun ladabtar da ma'aikata kan cewa a dakatar da Chief Justice na Nigeria, Honourable Justice Walter Nkanu Samuel Onnoghen kafin ta kammala bincike a kan tuhumar da ake masa na almundaha da kudaden.
Wasu shaidu sun nuna cewa akwai kudade masu yawa da suka shiga asusan ajiya na alkalin alkalan wadanda ya kasa bayanin inda suka fito.