Najeriya : Kasashen Turai, Sun Damu Da Korar Shugaban Kotun Koli
(last modified Sat, 26 Jan 2019 16:21:56 GMT )
Jan 26, 2019 16:21 UTC
  • Najeriya : Kasashen Turai, Sun Damu Da Korar Shugaban Kotun Koli

Tawagar masu sanya ido ta kasashen turai a zaben Najeriya, ta nuna damuwarta dangane da korar shugaban kotun kolin kasar a daidai lokacin da ya rage 'yan makwanni a gudanar da babban zaben kasar.

Amurka ma a wata sanarwar da ofishin jekadancinta a Najeriya ya fitar ta ce, ta damu kan dakatarwa da kuma sauya shugaban kotun kolin kasar, ba tare da amincewar majalisa ba.

A jiya Juma'a ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar, ya dakatar da aikin shugaban kotun kolin kasar, M. Walter Onnoghen, matakin da 'yan adawa na kasar suka danganta da mulkin kama karya, a kasa da wata guda da zaben shugaban kasar, wanda shugaba Buharin ke neman wani wa'adin mulki.

Tuni dai  Buhari ya nada Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin shugaban kotun kolin kasar na riko har sai an kammala shari'ar koraren alkalin alkalan, Onnoghe da ake tuhuma da kin bayyana dukiyar da ya mallaka kafin rantsar da shi a shekara 2017.

Shugaban ya bayyana cewa kotun da'ar ma'aikata ce ta bayar da umarni a dakatar da shi har sai an kammala gudanar da shari'arsa.