Sudan : Kungiyoyi Sun Yi Kiran Zanga Zanga Cikin Dare
Kungiyoyin kwadago a Sudan, sunyi kiran gudanar da zanga zanga cikin daren yau Asabar da kuma ranaku masu zuwa.
Wata sanarwa da kungiyar data hada ma'aikatan asibitoci, injiniyoyi da kuma malaman manyan makarantu ta fitar, ta bukaci al'umma a duk fadin kasar dasu gudanar da zanga zanga a yankunansu a cikin daren yau Asabar.
Kungiyar ta kuma kirayi 'yan Sudan dasu gudanar da zaman dirshin, a anguwanninsu a gobe Lahadi, sannan kuma su fito wata zanga zanga a ranar Laraba mai zuwa.
Tun a ranar 19 ga watan Disamba da ya gabata ne kasar Sudan ke fama da zanga zanga wacce ke da nasaba da tsadar rayuwa wacce yanzu ta rikide zuwa kyammar gwamnatin Shugaba Umar Hassane Al'Bashir wanda ke mulkin kasar yau kusan shekaru 30, bayan wani juyin mulki a shekara 1989.
Alkalumman da hukumomin kasar suka fitar sun nuna cewa mutum 30 ne suka mutu tun soma zanga zangar, saidai a cewar wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama mutane akalla 40 ne suka mutu a boren, a yayin da bangaren 'yan adawa na kasar ke cewa mutanenn da suka rasa rayukansu tun soma zanga zangar ya kai 50.