An Rantsar Da Alkalan Kotunan Zabe Mai Zuwa A Tarayyar Najeriya
Mukaddashin Alkalin Alkalai na Najeriya ya rantsar da alkalai da masu taimaka masu 250 na kotunan sauraron koke=koken zabubbuka masu zuwa .
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa mukaddashin alkalin alkalan Najeriya mai shari'a Tanko Muhammad ya yi kira ga alkalai da masu taimakamasu 250 na kutunan sauraron koke-koke a zabubbuka mai zuwa a kasar da su ji tsaron Allah a ayyukansu.
Mai shari'a Mohammad ya kara da cewa ma'aikatar shari'a a kasar tana cikin jarrabawa mai tsanani, don haka ya bukaci alkalan da mataimakansu su yi aikinsu tsakaninsu da Allah a koke-kuken da za'a gabatar masu a zaben na wannan shekara ta 2019.
Masu shari'a 15 ne suka halarcin bikin rantsar da alkalan da kuma mataimakansu a Abuja, sannan Mai shari'a Sidi Bage na daga cikin wadanda suka halarci bikin.
A jiya ne shugaban Mohammadu Buhari ya rantsar da Mai shari'a Tanko Muhammad a matsayin mukaddashin alkalin alkalan kasa, bayan da ya sauke wanda ya gada saboda matsalolin sahria da yake fuskanta.