Ma'aikatan Kiwon Lafiya Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Jamhuriyar DR Congo
Ma'aikatan kiwon lafiya sun gudanar da zanga-zangar lumana a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo domin bayyana matsalarsu ta rashin tsaro a yankunan da suke gudanar da ayyuka.
Ma'aikatan kiwon lafiya da suka fito daga asibitoci fiye da ashirin da biyar ne a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suka gudanar da zanga-zangar lumana a jiya Talata domin bayyana kokensu ga mahukuntan kasar kan rashin matakan tsaro a yankunan da suke aiki.
A sakon wasika da suka gabatar da ma'aikatar lafiya ta kasar bayan kammala zanga-zangar lumanar sun jaddada rashin matakan tsaro a yankunansu lamarin da ke barazana ga rayukansu, haka nan rashin kayayyakin aiki domin kula da lafiyar majinyata.