Mutum 4 Sun Hallaka Yayin Zanga-Zangar Dalibai A D/Congo
Hukumomin jamhoriyar Demokaradiyar Congo sun sanar da mutuwar mutum 4 yayin gudanar da zanga-zangar dalibai a kudu maso gabashin kasar
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto hukumomin kasar Congo na cewa a jiya lahadi daliban jami'o'in UNILU da Lubumbashi dake kudu masu gabashin kasar sun gudanar da zanga-zangar neman gwamnati ta biya musu wasu bukatunsu, to saidai a yayin da 'yan sanda suka yi kokarin tarwatsa su, zanga-zangar ta rikide zuwa dauki ba dadi tsanin daliban da 'yan sandar, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar dalibai 3 da dan sanda daya.
A cewar shaidu,daliban sun je fadar gwamnatin jahar Lumumbashi, tare da neman gwamnati ta tabbatar musu da wutar lantarki gami da tsabtaceccen ruwan sha a jami'o'i da kuma wurin kwanansu, sannan kuma tayi musu karin alawus-alawus nasu, saidai a yayin da suke kokarin komawa zuwa jami'o'insu sai suka ci karo da jami'an tsaro na 'yan sanda, inda suke yi ta halbinsu da hayaki mai sanya hawaye.
Tuni dai gwamnatin ta Congo ta ce za a gudanar da bincike kan dalilin da ya janyo wannan taho mu gama, kuma da zarar an kamala binciken, Ministan ilimi mai zirfi zai yi wa al'ummar kasar jawabi a game da sakamakon binciken.
An samu katse wutar lantarki da ruwa sha a jami'ar UNULI, ranar alhamis din da ta gabata, sanadiyar ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka yi wanda ya janyo ambaliyar ruwa a yankin.
Jami'ar UNILU dai na daga cikin manyan jami'o'in kasar Demokaradiyar Congo, inda a ko a shekarar bana, jami'ar ta dauki dalibai sama da dubu goma.