Kashi 14% Na Al'ummar Najeriya Na Tu'ammali Da Muggan Kwayoyi
Sakamakon wani bincike da aka gudanar a Najeriya ya yi nuni da cewa kashi 14,4 cikin dari na al'ummar kasar na tu'ammali da muggan kwayoyi.
Sakamakon binciken wanda aka gudanar hadin gwiwa da kungiyar tarayya turai da kuma hukumar MDD, mai yaki da muggan kwayoyi (UNODC) da kuma kuma gwamnatin Najeriya, ya nuna cewa jihar Lagos ce kan gaba a Najeriyar, da kashi 33%.
Hakan kuma a cewar binciken ya linka matsalaicin yawan masu tu'ammali da muggan kwayoyi a fadin duniya.
Binciken ya ce kamar sauren kasashen duniya, tabar wiwi ita ce aka fi tu'ammali da ita, baya ga dangin tramadol.
Yankin kudu maso yamma, shi sahun gaba wajen tu'amali da muggan kwayoyi a Najeriya a cewar binciken, inda kashi 22,4% na al'ummar yankin 'yan tsakanin shekara 15 zuwa 64 sukayi tu'ammali da kwaya a shekara data gabata.
Da yake sanar da sakamakon binciken, ministan kiwan lafiyar al'umma na Najeriyar, Osagie Ehanire, ya ce lamarin nada matukar daukan hankali, wanda dole a kara karfafa matakan yaki da matsalar, domin magance matsalolin da hakan ke haifar wa ga rayuwar al'umma da kiwan lafiya, da tsaro na kasar dake zaman mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.