Ivory Coast : An Daure Dan Majalisa Saboda Yada Labarin Karya
Wata kotu a Ivory Coast, ta daure wani dan majalisa saboda yada labarin karya.
Kotun ta daure dan majalisa Alain Lobognon, a zaman gidan kaso na shekara guda da kuma tarar kudin CFA 300,000 kan yada labaren karya, da kuma tada zaune tsaye, bayan wallafa wani labari a shaffin zama zumunta wanda ya janyo zanga zanga.
Saidai lauyen dan majalisar ya ce zasu daukaka kara kan hukuncin kotun, tare da danganta hukuncin da bita da kulin siyasa, kasancewar dan majalisar na kusa ne da shugaban majalsiar dokokin kasar, Guillaume Soro.
Hukuncin kotun daio na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin shugaban kasar ta Ivory Coast, Alassane Ouattara, ta yi tsami a watannin baya bayan nan tsakaninsa da shugaban majalisar dokokin kasar, Guillaume Soro.
A ranar Litini dai shugaba Ouatara ya sanar da shirin murabus din shugaban majalisar dokokin kasar, Guillaume Soro, a cikin watan Fabrairu mai shirin kamawa.