Jan 31, 2019 12:13 UTC
  • Sojojin Sudan Ba Za Su Bari Gwamnati Ta Fadi Ba

Babban Hafsan Sojan kasar Sudan Kamal Abdul-Ra'uf ya fada a yau alhamis cewa; Ba za su bari kasar ta shiga halin rashin tabbas ba

Kamal Abdul-Ra'uf ya kara da cewa; Ko kadan ba kuma za su bari kasar ta shiga hannun wasu mutane da suke damfare da kasashen waje ba

Shi ma ministan tsaron kasar ta Sudan, Iwadh Muhammad ya ce; Za su ci gaba da nuna goyon bayansu ga shugaban kasar Umar Hassan al-Bashir sannan ya kara da cewa: Sojojin kasar suna da cikakkiyar masaniya akan kulle-kullen da ake yi wa kasar ta Sudan da kuma yadda wasu suke fakewa da matsalar tattalin arziki da ake fama da shi."

 Ministan tsaron kasar ta Sudan ya kuma ce; Wasu mutane suna kokarin jawo sojojin kasar cikin abin da yake faruwa

Tun a ranar 19 ga watan Disamba na 2018 ne dai al'ummar kasar Sudan su ka fara Zanga-zangar kira ga shugaba Umar Hassan al-Bashir da ya sauka daga kan mukaminsa na shugabancin kasar.

Kawo ya zuwa yanzu fiye mutane 40 ne su ka rasa rayukansu kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa su ka ambata

Tags