Sudan : Malaman Jami'a Sun Shiga Cikin Masu Neman Sauyi
Malaman Jami'o'i a kasar Sudan Kimani 300 ne suka gudanar da zanga-zanga a tsakiyar Jami'a a birnin Khartun inda suke bukatar sauyin shugabanci a kasar.
Tashar talabijin ta France 24 ta bayyana cewa a yan Alhamis ne malaman jami'a kimani 300 suka gudanar da zanga-zanga na neman shugaban kasar Umar Hassan Albashir ya yi murabus .
Labarin ya kara da cewa Mamdoh Muhammad Hassan kakakin malaman jami'an ya bayyana cewa ba zasu amince da wani abu banda murabus na shugaban kasa ba.
A wani bangaren kuma jam'iyyun adawar kasar ta Sudan sun bukaci jam'iyyar mai mulkin kasar ta dakatar da shirinta na sauya kundin tsarin mulikin kasar don bawa shugaba Umar Hassan Albashir damar sake shiga takarar zabe na shekara ta 2020.
Tun ranar 19 ga watan Dece. shekarar da ta gabata ce mutanen Sudan suka fara zanga zangar kin jin gwamnatin kasar. Sannan ya zuwa yanzu an kashe mutane fiye da 40 a yayinsa gwamnatin kasar ta bada sanarwan a sake mutane fiye da 800 da ake tsare da su tun lokacin.