An Bude Iyakar Tsakanin Sudan Da Eritrea
(last modified Fri, 01 Feb 2019 03:27:56 GMT )
Feb 01, 2019 03:27 UTC
  •  An Bude Iyakar Tsakanin Sudan Da Eritrea

Shugaba Umar Hassan El-Bashir, na Sudan, ya sanar da sake bude iyakar dake tsakanin kasar da Eritrea.

Shugaban ya sanar da hakan ne a wani ganganmi da yake halarta tun daga jihar Kassala dake gabashin kasar mai raba iyaka da Eritrea, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya rawaito.

Gidan talabijin din aksar ya rawaito shugaba El'Bashir na cewa '' Siyasa zata iya raba mu, amma 'yan Eritrea, suna a matsayin 'yan uwanmu da iyayenmu har kullun, saidai ba tare da yin karin haske ba kan daukar matakin sake bude iyakar ba. 

Yau shekara guda da wannan iyaka ke rufe, sakamakon kafa dokar ta baci a jihar ta Kassala, a wani mataki na shawo kan matsalar 'yan daba, da masu safara mutane tun daga yankin kahon Afrika zuwa Turai.

Sake bude iyakar dake tsakanin kasashen biyu, zata taimaka wa dubbun dubatar mutane gudanar da ayyuka na dogaro da kai.

Wani jami'in  hukumar kula da 'yan gudun hujira ta MDD, (OIM), ta fitar sun nuna cewa, kimanin 'yan gudun hijira 100,000 suka bi ta Sudan a cikin shekara 2016, wadanda galibinsu, 'yan Eritrea ne.