ICC Zatayi Zama Bayan Watsi Da Bukatar Sallamar Gbagbo
A wani lokaci yau Juma'a ne, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, (ICC), zatayi wani zama kan bukatar da mai shigar da kara na kotun na ci gaba da tsare da tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, bayan da a kwanakin baya kotun ta yi watsi da hukuncin da alkalan kotun suka yanke na sallamarsa.
A ranar 15 ga watan Janairun da mukayi ban kwana dashi ne, alkalan kotun ta ICC, suka bukaci kotun data sallami Mista Laurent Gbagbo da na hannun damansa Charles Blé Goude, ba tare da wata wata ba, bayan wankesu daga tuhume tuhumen da ake masu na cin zarafin bil adama.
A zaman na yau, alkalan kotun daukaka kara zasu saurari mai shigar da kara na kotun, da wakilan mutanen da aka ci zarafinsu, da kuma lauyoyin MM. Gbagbo din da kuma Blé Goudé, inda kuma zata yanke hukunci kan ci gaba da tsare tsaffin jami'an biyu har zuwa wata shari'a bisa daukaka kara, ko kuma ta sallamesu bisa sharadi ko kuma ba tare da sharadi ba.
M. Gbagbo, wanda shi ne wani tsohon shugaban kasa na farko da aka gurfanar a gaban kotun ta ICC, ana zarginsa da laifukan cin zarafin bin adama a tarzomar data biyo bayan zaben kasar a tsakanin 2010 zuwa 2011, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu uku a cikin watanni biyar.
Tsohon shugaban kasar ta Ivory Coast, ya kwashe shekaru bakai a hannun kotun ta ICC dake birnin Hague.