An Tsarkake Wani Yanki Na Kudancin Libiya Daga Hanun 'Yan Ta'adda.
(last modified Fri, 01 Feb 2019 13:25:05 GMT )
Feb 01, 2019 13:25 UTC
  • An Tsarkake Wani Yanki Na Kudancin Libiya Daga Hanun 'Yan Ta'adda.

Dakarun tsaron kasar Libiya sun samu nasarar tsarkake wani yankin na jahar Sabaha dake kudancin kasar tare kuma da kame wani komandan 'yan ta'addar ISIS

Tashar talabijin din Al-alam dake watsa shirye-shiyenta da harshen Larabci daga nan kasar Iran ta habarta cewa a ranar Alhamis da ta gabata dakarun tsaron kasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'adda daga yankin Gadwah na jihar Sabaha dake kudancin kasar.

Dakarun tsaron Libiya sun sanar da cewa a yayin da suka tunkari yankin na Gadwah, ganin cewa mayakan 'yan ta'addar ba su da karfin tunkarar sojojin kasar sai suka arce daga yankin.

A wata sanarwa da ya fitar jiya alhamis, mai magana da yawun rundunar tsaron kasar ta Libiya Ahmad Mismari, a halin da ake ciki yanzu mafi yawan yankunan na jihar Sabaha na karkashin ikon Dakarun tsaron na Libiya.

Dakarun tsaron Libiya sun tabbatar da cewa tsarkake yankin na Gadwah na daga cikin ayyukan tsarkake kudancin kasar da jami'an tsaron kasar suka fara tun daga ranar 17 ga watan janairu na wannan shekara ta 2019.

Har ila yau dakarun tsaron Libiya sun sanar da cewa a jiya alhamis din sun samu nasarar cabke Khalifa al-Barq daya daga cikin komondojin kungiyar ta'addancin nan ta ISIS a garin Sirte.

Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin matsalar tsaro, bayan da kungiyar tsaron Nato da sojojin Amurka suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayyi kanal Mu'amar kaddafi.