Belgium Ta Amince Karbar Tsohon Shugaban Ivory Coast
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35052-belgium_ta_amince_karbar_tsohon_shugaban_ivory_coast
Kasar Belgium, ta bayyana amincewa da karbar tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta amince da sallamarsa.
(last modified 2019-02-02T15:58:16+00:00 )
Feb 02, 2019 15:58 UTC
  • Belgium Ta Amince Karbar Tsohon Shugaban Ivory Coast

Kasar Belgium, ta bayyana amincewa da karbar tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta amince da sallamarsa.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Belgium din ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, an amince da karbar Mista Gbagbo, ne saboda alakar iyalai da yake da ita da kasar.

Kuma a cewarsa hakan yana daga cikin goyan bayan da suke baiwa kotunan kasa da kasa, saidai bai bayyana ko har Mista Gbagbo din ya riga ya isa kasar ta Belgium ba ko kuma a'a.

A Jiya Juma'a ne kotun ta ICC ta amince da sakin tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo da tsohon na hannun damansa kuma shugaban matasan Jam’iyyarsa, Charles Ble Goude, bisa sharadi, ciki harda na samarda kasarsa da zata karbe su, sannan kuma ba zasu koma kasarsu ba, ko kuma tafiya wata kasa ba, har sai da amincewar kotun, kana kuma ba zasu yi wani bayyani ga manema labarai ba, kamar yadda kuma ba zasu tattauna da shaidun shari'ar da aka masu ba.

Hukuncin kotun na zuwa bayan bukatar hakan da gungun masu shigar da kara a kotun suka gabatar.

Alkalan kotun da ke birnin Hague sun wanke tsaffin jami'an na Ivory Coast saboda abinda suka kira rashin kwakkwarar shaidar da za ta sa a daure su.

An dai tuhumi mutanen biyu ne da hannu da tarzomar bayan zaben kasar tsakanin shakarar 2010 zuwa 2011 wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane akalla 3,000 bayan zaben wanda aka sanar da Alhassan Ouattara ya samu nasara.