An Jinkirta Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniya Sulhu A Afrika Ta Tsakiya
A Sudan an jikirta bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin gwamnati da gungun kungiyoyi masu dauke da makamai a Jamhuriya Afrika Tsakiya.
Jiya Lahadi ne aka tsara bangarorin zasu daddale yarjejeniyar da suka cimma a birnin Khartoum, saidai an ce an dage bikin har zuwa gobe Talata, saboda wasu shuwagabannin kasashen Afrika da zasu halarci bikin.
Daga cikin shuwagabannin da ake sa ran zasu halarci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar akwai shugaban kasar ta Afrika ta tsakiya, Faustin Archange Touadéra, dana kasar Sudan Umar Hassan Al-Bashir da takwaransa na Chadi Idriss Deby.
A Ranar Asabar data gabata ne kungiyar tarayya Afrika ta sanar da cewa an cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Afrika ta tsakiya da kuma wasu gungun kungiyoyi masu dauke da makamai 14 na Afrika ta tsakiya bayan shafe kwanaki goma na tattaunawa a birnin Khartoum na kasar Sudan, saidai ba tare da yin karin haske ba.
Amma wasu majiyoyi sun ce yarjejeniyar ta tanadi yin afuwa wa wasu jagororin kungiyoyin masu dauke da makamai wanda gwamnatin kasar ta ki amincewa dashi a cen baya, da kuma kafa rundinar tsaro ta hadin gwiwa. a
Ana da dai kyakyawan fata ga wannan yarjejeniyar, wacce ita ce irinta ta takwas da aka cimma a wannan kasar ta Jamhuriya Afrika ta Tsakiya inda gungun kungiyoyi masu dauke da makamai ke rike da kashi 80% na fadin kasar.