Guinea : Mutane Takwas Suka Mutu Bayan Sake Bullar Ebola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3508-guinea_mutane_takwas_suka_mutu_bayan_sake_bullar_ebola
Alkalumen da hukumar yaki da cutar Ebola a kasar Guinea ta fitar na cewa mutane takwas ne cikin tara da akayi rejistan su suka mutu sanadin kamuwa da cutar ta Ebola.
(last modified 2018-08-22T06:58:05+00:00 )
Apr 06, 2016 23:36 UTC
  • Guinea : Mutane Takwas Suka Mutu Bayan Sake Bullar Ebola

Alkalumen da hukumar yaki da cutar Ebola a kasar Guinea ta fitar na cewa mutane takwas ne cikin tara da akayi rejistan su suka mutu sanadin kamuwa da cutar ta Ebola.

kakakin hukumar Ibrahima Sylla ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa mutun na karshe daya mutu sanadin cutar wata mata ce dake jinyar cutar a cibiyar CTE dake N'zerekore a birni mafi girma na kudancin kasar.

kawo yanzu dai a cewar hukumar mutun daya ne ya yi saura cikin wadanda ake sa ma ido sanadin kamuwa da cutar duk sauran guda takwas sun riga mu gidan gaskia.

Dama kafin hakan hukumar lafiya ta duniya ta sanar da mutuwar mutane bakwai cikin takwas da aka yi rejistan su tun bayan sanarwar sake bullar cutar a ranar 17 ga watan Maris daya gabata.