Najeriya: 'Yan Bindiga Sun Kai Wasu Sabin Hare-Hare A Jihar Zamfara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35090-najeriya_'yan_bindiga_sun_kai_wasu_sabin_hare_hare_a_jihar_zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, in da suka kashe mutane da dama tare da kona gidajensu a garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Gusau.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Feb 05, 2019 11:50 UTC
  • Najeriya: 'Yan Bindiga Sun Kai Wasu Sabin Hare-Hare A Jihar Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, in da suka kashe mutane da dama tare da kona gidajensu a garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Gusau.

Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai  cewa, jami’an tsaro sun gaza ba su kariya duk da cewa, an tura wani jirgin saman soji da ya dauki lokaci yana shawagi a yankin da aka kai farmakin.

Jami'an tsaron sun bukaci mazauna yankin da su yi ta kansu kamar yadda rahotanni ke cewa.

kawo yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba a hare-haren na baya-bayan nan, amma rahotanni na cewa, daga cikin wadanda aka kashe har da ‘yar uwar Sanata Kabiru Marafa da maharan suka yi awon gaba da mijinta.

Jihar Zamfara ta jima  tana fuskantar hare-hare daga maharan da ake zargi 'yan fashi ne da barayin shanu.

Masu sharhi kan harakokin  tsaro na ganin matakan da gwamnati take dauka ba su yi wani tasiri ba na hana ci gaba da kai hare-hare a jihar.