Feb 05, 2019 11:53 UTC
  • Ministan Tsaron Sudan Ya Gargadi Masu Adawa Da Gwamnati

Ministan tsaron kasar Sudan ya ce jami'an tsaro ba za su laminta wasu mutane su jefa kasar cikin kaka nike ba

Tashar talabijin din Al-hadas ta nakalto ministan tsaron kasar Sudan Awad ibn Owf a wannan talata na cewa dakarun tsaron kasar na goyon bayan kundin tsarin milkin kasar, kuma ba za su bari wasu mutane su jefa kasar cikin mawuyacin hali saboda amfanin kansu ba.

Ministan ya kara da cewa abubuwan da suka faru a baya-bayan tsakanin matasa , har ma da masu yawan shekaru da kuma  wasu daga cikin iyalan kasar, na nuni da cewa ya zama wajibi ga gwamnati ta sake yin nazari da kuma gyara dokar kasar wanda hakan zai bata  damar daukan dokar ba sani ba sabo a kan masu zanga-zangar.

A jiya Litinin ne al'ummar kasar sudan suka sake gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna adawa da mawuyacin halin da kasar ta shiga na tattalin arziki a gariruwan daban daban na kasar cikin kuwa harda Khartum babban birnin kasar tare da neman shugaba Omar Al-bashir ya yi murabus daga kan mikaminsa.

A yayin gudanar da zanga-zangar, jami'an tsaro na 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa mahalarta zanga-zangar.

Tun a ranar 19 ga watan Dicembar shekarar 2018 din da ta gabata ne al'ummar kasar Sudan suka fara zanga-zangar nuna adawa da kara farashin kudin man fetir da biredi, da kuma mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ya shiga.

Tags