CRA : An Cimma Yarjejeniya Tsakanin Gwamnati Da Masu Dauke Da Makamai
-
PHOTO © ASHRAF SHAZLY / AFP
Gwamnatin Jamhuriya Afrika ta tsakiya da gungun masu dauke da makamai a kasar sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a wani buki da aka gudanar yau a Kahrtoum babban birnin aksar Sudan.
Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da gungun masu dauke da makamai 14, ta tanadi kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru anayi a wannan kasa ta jamhuriya Afrika ta tsakiya.
Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halartar shugaban kasar ta RCA Faustin Archange Touadéra, da takwaransa na Sudan Umar Hassan El-Bashir, da kuma shugaban kwamitin kungiyar tarayya Afrika, Musa Faki Mahamat.
Har kawo yanzu dai ba'a fayyace hakikanin abunda yarjejeniyar ta kunsa ba, saidai wasu majiyoyin sun ce yarjejeniyar ta tanadi yin afuwa wa jagororin kungiyoyin masu dauke da makamai, raba mukamai na gwamnati da kuma shigar da tsaffin mayaka cikin aikin jami'an tsaro.
An dai ki bayyana abunda yarjejeniyar ta kunsa ne don kada a samu rarrabuwar kai ko matsin lamba kan bangarorin.
Nan gaba za'a gudanar da wani taro a Bangui babban birnin kasar, inda za'a fayyace wa 'yan kasar abunda yarjejeniyar ta kunsa.