Jami'an Tsaro A Kasar Sudan Sun Kama Babbar Sakatariyar Jam'iyyar Umma
(last modified Wed, 06 Feb 2019 06:44:10 GMT )
Feb 06, 2019 06:44 UTC
  • Jami'an Tsaro A Kasar Sudan Sun Kama Babbar Sakatariyar Jam'iyyar Umma

Majiyar jam'iyyar Umma ta kasar Sudan ta bada sanarwan cewa a jiya Talata da dare jami'an tsaron kasar sun kama babban sakataren jam'iyyar Ummu Salma Assadikul Mahdi babban sakataren kungiyar da kuma Saratu Naqdullah wata yar jam'iyyar.

Tashar talabijin ta Al-alam nan birnin Tehran ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar ta Sudan sun kama wadannan mutane biyu ne a dai-dai lokacinda suke zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Umar Hassan al-bashir a tsakiyar birnin Khartum babban birnin kasar.

Jam'iyyar Umma dai ita ce jam'iyyar adawa mafi girma a kasar ta Sudan. Jam'iyyar ta kara da cewa a lokacin kama wadannan manya-manyan jam'iyyar sun yi dirar mikiya a kan masu zanga-zanga sannan suka kama wadanda suka kama. 

Tun ranar 19 ga watan Decemban shekarar da ta gabata ce gwamnatin kasar Sudan take fuskantar matsalar masu adawa da shugabancin shugaba Umar Hassan albashir. 

Kafin haka dai farashin kayakin abinci musamman Bridi sun kara tsada sannan sauran kayakin bukatu na yau da kullum ma sun yi tashin goron zabi.