Ivory Coast : ICC Ta Mika Gbagbo Ga Hukumomin Belgium
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35106-ivory_coast_icc_ta_mika_gbagbo_ga_hukumomin_belgium
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta mika wa hukumomin Belgium, tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, bayan da kotun ta sallame shi a ranar 1 ga watan nan.
(last modified 2019-02-06T05:27:57+00:00 )
Feb 06, 2019 05:27 UTC
  • Ivory Coast : ICC Ta Mika Gbagbo Ga Hukumomin Belgium

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta mika wa hukumomin Belgium, tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, bayan da kotun ta sallame shi a ranar 1 ga watan nan.

Laurent Gbagbo wanda kotun ta wanke game da tuhumce tuhumcen da ake masa, ya bar kasar Hollande da yammacin jiya Talata, bayan da kotun ta mika shi ga hukumomin na Belgium.

Kotun dai ta sallame shi ne bisa sharudda, wadanda suka hada da hana shi komawa kasarsa da kuma kin yi wani bayyani ga manema labarai.

Belgium ta ce ta amince da karbar Mista Gbagbo, ne saboda alakar iyalai da yake da ita da kasar, da kuma huldar dake tsakaninta da kotun ta ICC.

Alkalan kotun da ke birnin Hague sun wanke tsahon shugaban kasar ta Ivory Coast, Luarent Gbagbo da kuma tsohon na hannun damansa Charle Ble Goude, saboda abinda suka kira rashin kwakkwarar shaidar da za ta sa a daure su.

An dai tuhumi mutanen biyu ne da hannu a tarzomar bayan zaben kasar na tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011 wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane akalla 3,000.