'Yan Gudun Hijirar Najeriya A Kasar Kamaru Suna Da Bukatar Taimako
(last modified Wed, 06 Feb 2019 19:25:45 GMT )
Feb 06, 2019 19:25 UTC
  • 'Yan Gudun Hijirar Najeriya A Kasar Kamaru Suna Da Bukatar Taimako

Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa; Wajibi ne ga kungiyoyin ba da agaji da suke karkashin Majalsiar su kara ba da taimako ga 'yan hijirar Najeriya a kasar Kamaru

kakakin Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar Stéphane Dujarric ya bayyana cewa; Taimakawa 'yan gudun hijirar ya zama wajibi, domin 'yan gudun hijirar suna taraddudin komawa kasarsu saboda rashin tsaro."

Stéphane Dujarric ya kuma ce ana samun yin aiki tare a tsakanin ma'aikatan agajin da kuma jami'an gwamnatin kasar ta Kamaru.

Bugu da kari Stéphane Dujarric ya yi ishara da cewa; Da akwai mutane dubu 35 da su ka tsallaka iyaka daga Najeriya zuwa kasar ta Kamaru.

Har ila yau,Stéphane Dujarric ya ce Daga fara rikicin na Boko haram na 2009 adadin wadanda suka zama 'yan gudun hijira sun kai miliyan biyu da dubu dari shida. Bugu da kari rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 20.