Amurka Ta Dakatar Da Baiwa Kamaru Tallafin Soji
Amurka ta sanar da soke tallafin soji da take baiwa Jamhuriya kamaru, bisa zargin jami'an tsaron kasar da mummunan toye hakkin bil adama.
Hukumomin na Amurka sun ce sun dau matakin ne bisa samun rahotanni cin zarafin bil adama da ake zargin sojojin na Kamaru da aikatawa, tare da bukatar hukumomin na Yaoude dasu gudanar da bincike kan batun wanda suka ce sahihi ne, domin gurfanar da wadanda keda hannu a wannan aika aika.
Shirin da Amurka ta soke ya shafi horo da kuma wasu kayayakin jigaren soji na dakon kaya na Amurka kirar C-130 da rundinar sojin sama na kamaru ke amfani dasu.
Haka zalika da soke shirin baiwa Kamarun tallafin wasu jigaren ruwa hudu na sintiri da kuma wasu motoci masu sulke, da kuma soke kasar ta Kamaru daga cikin takara wani shiri na baiwa sojoji horo.
Kawo yanzu dai hukumomin na Kamaru basu maida martani ba kan wannan matakin na Amurka.
A jiya Alhamis ne wasu gomman kungiyoyin masu zaman kansu suka bukaci MDD, data gudanar da bincike kan zargin taye hakkin bil adama a yankin masu magana da turancin ingilishi dake yankin arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma na Kamaru.