Gobara Ta Cinye Wani Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35129-gobara_ta_cinye_wani_sansanin_'yan_gudun_hijira_a_najeriya
Rahotanni daga Najeriya na cewa wata mummunar gobara ta cinye wani sansanin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2019-02-08T04:45:41+00:00 )
Feb 08, 2019 04:45 UTC
  • Gobara Ta Cinye Wani Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa wata mummunar gobara ta cinye wani sansanin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin kasar.

Bayanai sun ce akwai yara da dama da gobara data auku a jiya Alhamis ta rutsa dasu a sansanin na Monguno dake jihar Borno.

Babu dai karin bayyani kan musababin tashin gobarar.

Mazauna yankin sun ce gobara ta fara ne da misalin karfe 12 na rana agogon wurin tare da kone dun wurin.

Sansanin dai ya kunshi daruruwan 'yan gudun hijira da suka tserewa rikicin boko haram a yankin tafkin Chadi.

An dai jima ana samun gobara a sansanin 'yan gudun hijira na Monguno, musamman a lokacin rani da iska.

Rikicin boko haram wanda ya tsananta a baya bayan nan ya hadassa kaurar mutane kimanin 60,000 a cikin watanni uku da suka gabata a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD.