Sudan : Mutane 130,000 Suka Yi kaura Saboda Rikici A Jebel Marra
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3514-sudan_mutane_130_000_suka_yi_kaura_saboda_rikici_a_jebel_marra
MDD ta bayana cewa sama da mutane dubu dari da talatin ne, suka yi kaura saboda rikicin daya ki yaki cinyewa tsakanin sojoji da 'yan tawaye a Jebel Marra dake yankin Darfour a yammacin kasar Soudan
(last modified 2018-08-22T06:58:05+00:00 )
Apr 07, 2016 00:34 UTC
  • wani sansanin \'yan gudun hijira a Soudan
    wani sansanin \'yan gudun hijira a Soudan

MDD ta bayana cewa sama da mutane dubu dari da talatin ne, suka yi kaura saboda rikicin daya ki yaki cinyewa tsakanin sojoji da 'yan tawaye a Jebel Marra dake yankin Darfour a yammacin kasar Soudan

Alkaluma da kungiyoyin jin kai a wannan kasa suka fitar sun nuna cewa daga karshen watan Maris daya gabata akalla mutane dubu dari da talatin da takwas ne suka kauracewa yankin.

A halin da ake ciki a cewar Herve Ladsous wani babban jami'in samar da zamen lafiya na MDD a wannan yankin ana ci gaba da gwabza fada da barin wuta ba kakkautawa a yankin na Dafour.

Mr Herve na bayana hakan ne a zauran kwamitin tsaro na MDD a wani taro na bitar halin da ake ciki a yankin na Darfour.

wani kiyasti da MDD tayi ya nuna cewa tun daga 2003 kawo yanzu, rikicin yankin Darfour dai yayi sanadin mutuwar mutane sama da 300,000 tare da cilastawa sama da Miliyan 2,6 kauracewa gidajen su