Al'ummar Kasar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati
(last modified Sat, 09 Feb 2019 05:28:46 GMT )
Feb 09, 2019 05:28 UTC
  • Al'ummar Kasar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati

A jiya juma'a al'ummar kasar Sudan sun sake gudanar da zanga-zangar kin gwamnati a jihohin daban daban na kasar ciki harda Khartoum babban birnin kasar

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya habarta cewa mahalarta zanga-zangar sun yi ta rera taken neman shugaba Omar Al-bashir ya sauka daga kan karagar milki, saidai jami'an tsaron kasar sun kai musu farmaki tare da tarwatsa su ta hanyar harba musu hayaki mai sanya hawaye.

Wannan zanga-zanga na zuwa ne a matsayin amsa kiran gamayar kungiyar kwadago ta kasar, wacce ta kumshi kungiyoyin ma'aikan kiyon lafiya, da injiniyoyi, da malimam makarantun kasar.

Tun a ranar 19 ga watan Dicembar 2018 din da ta gabata ce al'ummar kasar Sudan suka fara gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ya shiga musaman yadda aka samu karin farashin man fetir da biredi, to saidai daga bisani zanga-zangar ta rikide zuwa ga kawo karshen gwamnatin Shugaba Al-bashir.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar Sudan ta sanar da mutuwar mutum 30 a yayin zang-zangar, to saidai kungiyar kare hakin bil-adama ta kasa da kasa cikin wani rahoto na musaman da ta gabatar ta sanar da cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu ya haura zuwa 40.

A wasu jihohin kasar, gwamnatin Sudan ta sanya dokar ta bace, lamarin da ya sanya aka rufe wasu makarantu da jami'o'in kasar.