Kasar Masar Ta Karbi Shugabancin Karba-Karna Na Tarayyar Afrika
(last modified Mon, 11 Feb 2019 11:19:40 GMT )
Feb 11, 2019 11:19 UTC
  • Kasar Masar Ta Karbi Shugabancin Karba-Karna Na Tarayyar Afrika

Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya karbi shugabancin karba-karba na kungiyar Tarayyar Afrika.

Tashar talabijin ta "Alhadath" ta bayyana cewa shugaban kasar ta Masar ya karbi shugabancin kungiyar tarayyar ta Afrika ne da shi'arin warware matsalolin yan gudun hijira, masu neman mafaka da kuma kauran mutanen nahiyar a dole zuwa wasu nahiyoyi.

Wannan shi ne karon farko kenan wanda kasar Masar take karban shugabancin kungiyar ta AU tun bayan kafuwarta a shekara ta 2002.

A cikin jawabinsa na karban shugabancin kungiyar Shugaban Abdulfattah Assisi ya bayyana cewa dole ne  a kauda duk wani shinge wanda yake hana kasashen kungiyar aiki tare don warware matsalolinta.

Tun jiya Lahadi ce aka fara taron shuwagabannin kasashen na Afrika a birnin Adis'ababa na kasar Ethiopia. A wannan taron dai shuwagabannin zasu tattauna batun fadada huldar tattalin arziki tsakanin kasashen kungiyar, matsalolin tsaro a nahiyar, samar da kudaden aiki, da kuma kammala batun samar da yanki kasuwanci wanda yake na kowa a nahiyar.