PDP Ta Yi Tsokaci Kan Gobarar Ofishin INEC
Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana kaduwarta game da gobarar da ta cinye kayayyakin zabe a ofishin Hukumar Zaben Kasar, INEC da ke yankin Quan Pan a Jihar Filato, in da ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.
An kona daya daga cikin ofishin hukumar zabe a Najeriya kwanaki shida kacal kafin gudanar da babban zabe a kasar, gobarar dai ta faru ne a ofishin hukumar a jihar Filato dake arewacin kasar inda muhimman kayayyakin zabe kamar akwatuna da takardun jefa kuri'a suka kone.
Mai magana da yawun hukumar ya bayyana kona ofishin a matsayin mayar da hannun agogo baya a bangaren shirye-shiryen zabe.
A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar ta bayyana cewa wannan ne karo na biyu da aka samu konewar ofishinta a cikin wannan watan, inda tayi kira ga jami'an tsaro a kasar da su kara matsa kaimi wajen ba ofisoshinsu tsaro.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, PDP ta bayyana tashin gobarar a matsayin wani bakon abu a daidai lokacin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da zaben shugabancin kasar.
PDP ta dika ayar tambaya kan makomar mutanen da katunan zabensu suka kone a wannan gobarar, lura da cewa akasarinsu sun shirya karbar katunan a ranar Litinin.
Kimanin katunan zaben dubu 7 suka kone a gobarar, yayin da Hukumar INEC ta bukaci jami’an ‘yan sanda da su tsananta tsaro a sauran ofisoshinta da ke sassan kasar.