Tsohon Shugaban Amurka Ya Zanta Da Shugaba Buhari Ta Wayar Tarho
Tsohon shugaban kasar Amurka billClinton ya santa da shugaban tarayyar Najeriya Muahmadu Buhari ta wayar tarho.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto Mr Femi Adesina mai bawa shugaban kasa shawara kan lamuran watsa labarai yana fadar haka a yau Alhamis.
Adesina ya ce shugaban Buhari ya zanta da tsahon shugaban kasar Amurkan ne a jiya Laraba, inda Mr Clinton ya bayyana uzurinsa na rashin halattan taron sanya hannu na yan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa wanda aka gudanar a Abuja. Ya kuma yi fatan za'a gudanar da zabubbuka na ranar Asabar 16 ga watan da sauransu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Kafin haka dai Mr Clinton ya yi alkawarin zai halarci bikin sanya hannu na amincewa a gudanar da zabe cikin zaman lafiaya a kasar, wanda yan takarar neman shugabancin kasa suke yi a ko wani zabe.
Adesina ya ce shugaban Buhari ya yabawa tsohon shugaban kasar na Amurka , sannan ya bayyana shi a matsayin mai sun alkhairi ga tarayyar Nageriya