Benin: Patrice Talon, Ya Yi Alkawarin Yin Wa'adin Mulki Guda
Sabon shugaban kasa Benin Patrice Talon ya yi alkawarin yin wa'adin mulki daya, kamar yadda yayi alkawari a yakin neman zaben sa.
Patrice Talon, wanda ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na ranar 20 ga watan Maris da ya gabata da kashi 65.37 % na kuri'un da aka kada, an rantsar da shi jiya a matsayin shugaban Benin jiya Laraba a Porto-Novo hedkwatar siyasar kasar.
Mr Talon ya kuma yi alkawarin girmama kundin tsarin mulkin kasar na tsawon wa'adin mulkinsa na shekaru biyar daga shekarar 2016 zuwa 2021, tare da kuma bayyana niyyarsa gaban mambobin kotun kolin kasar na cika alkawuran ayyukan kasa da aka mika masa, tare da girmama 'yancin dan adam.
kazalika sabon shugaban ya ce zai maida dukkan karfinsa ga ci gaban kasa da yaki da ta'adanci, da hadin kan kasa.