AFCON_U20 : Za'a Fafata A Wasan Karshe Tsakanin Senegal Da Mali
Da yammacin Yau Lahadi za a buga wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na matasa, tsakanin Senegal da Mali a filin wasa na Seyni Kounche da ke Yamai babban birinin Jamhuriyar Nijar.
Kafin hakan dai Najeriya ta rasa damar samun matsayi na uku a gasar, bayan fafatawa ta neman mataki na uku da Afrika ta Kudu, wanda ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da suka shafe mintuna 90 da karin lokaci ba tare da kowa ya jefa kwallo a ragar wani ba.
A zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gidan ne Afrika ta Kudu ta samu nasara kan Najeriya da kwallaye 5-3.
Najeriya dai tana cikin kasashen da matasansu samu ciri tikitin halartar gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 ta da kasar Poland za ta karbi bakunci a watan Mayu mai zuwa na wannan shekara.