Kisan Kiyashin Kajuru: Al-Rufa'i Ya Ziyarci Yankin
Gwamnan Jihar Kaduna Ahmad Al-rufa'i ya ziyarci yankin da aka yi kisan kiyashi na karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a jiya Asanbar inda ya ganewa idanunsa irin asarar da aka yi .
Jaridar Premuim Times ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnan ya kai ziyarar ne tare da rakiyar jami'an tsaro a jihar ta Kaduna, sannan mai bawa gwamnan shawara kan al-amuran watsa labarai Samuel Aruwa ya ce Faruk Yahaya kamandan sojojin Najeriya runduna ta daya ne yayi masa bayayin yadda suka gano gawawwakin mutane 66 a yankin Maruu da Iri na karamar hukumar ta Kajura.
Daga cikin wadanda suka yiwa gwamnan jihar rakiya akwai shugaban karamar hukumar Kajuru Cafra Caino da kuma daractan hukumar yansandan ciki na jihar A.I Koya.
Kwamishinan 'yansanda na jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman ya tabbatar da aukuwan kashe-kashen a ranar Jumma'an da ta gabata,.
Mutane da dama sun bayyana ra'ayinsu dangane da kisan, inda wasu suke zargin gwamnan da rashin bada sanarwan kisan sai ranar jumma'a bayanda an yi shi a ranar Lahadin da ta gabata.
Wasu kuma suna ganin shirin yan siyasa ne kawai na rikita zaben da aka shirya a kasar. inje jaridar Premium times.