Sudan Zata Fita Daga Matsalolin Da Take Fama Da Su_ Al-Bashir
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya bayyana cewa kasarsa zata fita daga matsalolin da take fama da su a halin yanzu.
Tashar talabijin ta Al-Hadath ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa gwamnatinsa tana shirye-shiryen ganin an kawo karshen zanga-zangar da mutanen kasar suke yi na kin gwamnatinsa, sannan zai warware matsalolin tattalin arzikin da kasar take ciki.
A wani bangaren na maganarsa a yau Lahadi, shugaba Umar Hassan Albashir ya bayyana cewa mutanen kasar Sudan suna hira da yan jaridu na kasa da kasa a inda suke sukan gwamnatinsa ba tare da wani ya tanka musu ba.
Sai dai a ranar jumma'ar da ta gabata ce karamin minista a ma'aikatar tsaron cikin gida Ma'amun Hassan Ibrahim ya ya barazanar amfani da karfi don murkushe yan adawar da suke kira zuwa ga sauya gwamnatin kasar.
Tun ranar 19 ga watan Decemban da ya gabata ne mutanen kasar Sudan suka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaba Umar Hassan Albashir saboda tsadar rayuwa a kasar.