Feb 19, 2019 12:22 UTC
  • Sojojin Najeriya Biyu Sun Kwanta Dama Sanadiyyar Fada Da Kungiyar Boko Haram

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaro na cewa; An sabon fadan ne a tsakanin sojojin kasar da kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabashin kasar a kusa da iyaka da kasar Kamaru

Majiyar ta ce sojoji biyu sun kwanta dama yayin da wasu shida su ka jikkata

A ranar asabar din da ta gabata ma dai kungiyar boko haram ta kai wani harin a kan wani masallaci da yake kusa da birnin Maiduguri a Jahar ta Borno. Mutane 8 ne su ka kwanta dama sanadiyyar wancan harin

A cikin kwanakin bayan nan kungiyar ta boko haram ta tsakanta kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin kasar, musamman a tsakanin jahohin Borno da Yobe

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe kungiyar ta boko haram, tun lokacin da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa shekaru 4 da su ka gabata

Kungiyar boko haram ta fara gudanar da kai hare-hare na ta'addanci ne dai tun a 2009 wanda ya zuwa yanzu ya ci rayuka mutane 20,000, yayin da wasu dubban dubata su ka jikkata.

Kididdiga ta tabbatar da cewa da akwai fiye da mutane miliyan 2 da su ka zama 'yan gudun hijira sanadiyyar hare-haren na Boko haram

 

Tags