UNICEF Ta Bayyana Muhimman Matakan Kare Yara A CRA
Feb 19, 2019 13:38 UTC
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya zayyana wasu matakan kare yara da ya kamata a dauka a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR.
Da yake yabawa yarjejeniyar zaman lafiya da bangarori 15 masu rikici suka sanyawa hannu a CAR, asusun UNICEF ya ce yanzu ne lokacin da ya kamata a yunkura, tare da fitar da matakan da ya kamata kungiyoyi masu dauke da makamai da hukumomin shari'a da gwamnati su dauka don kare makomar miliyoyin yara.
A cewar asusun, rikicin ya fi shafar yara, inda 1 cikin yara 4 ke rashin matsuguni a kasar da ba ta da iyaka da teku, ko kuma kasashe makwabta, yayin da har yanzu akwai miliyoyinsu da ba sa zuwa makaranta da fama da tamowa da cututtuka da cin zarafi da bauta.
Tags